Na Dawo Rakiyar Buhari – Sarkin Yakin Buhari

Daga Yau NI Abdul Ra’uf Matawalle (Sarkin Yakin Buhari) Na Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Karya Da Yaudara

A yau na kasance mai nadama da tuba ga Allah da kuma neman gafarar ‘yan uwana ‘yan Nijeriya baki daya soboda mun sanyawa mutane soyayyar wannan Bawan Allah shugaban kasa janaral Buhari ta hanyar karya da gaskiya.

Mun tallata shi duk a tunanin mu adali ne mai son talaka da kaunar talaka ne, sai dai kaico wallahi billahi a tarihin Nijeriya ba a taba gwamnati da bata kaunar talaka irin ta Buhari ba. Hawan sa mulki komai na tattalin arzikin kasar mu ya rushe, ga dinbin bashin bala’i da yake ta ciyowa.

Akalla daga hawa mulkin sa ya ciyo bashin naira na gugan naira har naira tiriliyan 32, kuma yanzu yana neman izinin sake ciyo wani bashin naira biliyan 500.

Wannan wace irin musifa ce? Allah mun tuba. y
Yunwa da talauci ya yi wa talaka katutu kullum fadi ake yi an karbo kudade daga hukumar hana cin hanci da rashawa. Amma wani mai Jar Dara ya lakume babu wani cigaba da muka tsinci kan mu sai kunci da yunwa da talauci da koma baya.

Wallahi ban taba zaton Buhari zai ci amanar talaka ba. Amma ya sani akwai Allah yana nan a madakata. Daga yau na sauka daga matsayin Sarkin yakin Buhari kuma muna neman yafiyar ‘yan Nijeriya da muka sanya ra’ayi da soyayyar sa da su yafe mana kuma zabe nangaba mu baiwa Allah zabi.

Wallahi babu wani mai gaskiya sai Allah da Manzon sa, sai masu kamantawa. Amma ba irin Buhari ba.

Related posts