Na Daina Jin Dadin Duniya Mutuwa Kawai Nake Jira – Aminu Dantata

Hamshaƙin Attajiri ɗan kasuwar nan na jihar Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya bayyana cewa a halin da ya ke ciki baya jin daɗin rayuwa.

Dantata, mai shekaru 91 a duniya, ya kuma ce shi babban burinsa shi ne ya cika da imani.

Dantata ya bayyana haka ne a jiya Talata yayin da ya karɓi baƙuncin mataimakin ɗan takarar mataimakin shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC, Kassim Shettima a gidansa da ke unguwar Koki a jihar Kano.

Ya ce a lokacin ƙuryciyarsa ya yi mu’amala da harkar kasuwanci da mutane masu yawan gaske wanda a yanzu abu ne mai wahala ya zayyano mutum goma da su ke raye.

“Na yi yawon fatauci a dukkanin jihohin Najeriya inda na yi mu’amala da mutane da mafi yawansu abokan cinikayyata ne a waɗannan jihohi. Sai dai abin takaici shi ne a cikin jerin waɗanda mu ka haɗu abu ne mai wahala in zayyano mutum goma da su ke da rai”

“Maganar gaskiya a halin yanzu ina jiran wa’adi ne domin bana jin daɗin rayuwa, burina in cika da kyau da imani” In ji Aminu Dantata.

Haka kuma hamshaƙin attajirin ya ƙara da cewa yana fatan duk wanda ya ɓata wa ya yafe masa shi kuma duk wanda ya yi masa ba daidai ba ya yafe masa.

Labarai Makamanta