Na Bar PDP Har Abada – Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, a ranar Asabar, ya bayyana cewa ba zai taba komawa jam’iyyar adawa ta PDP da siyasa ba gaba daya a rayuwarsa.

Ya bayyana hakan ne yayin hira da shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu da sauran masu fada a ji a jam’iyyar da suka ziyarcesa ranar Asabar bayan ganawar sirrin da suka yi, a gidansa dake birnin Abeakuta na jihar Ogun.

“Na fita harkar siyasa kuma babu abinda zai iya mayar da ni. Duk wanda ke son shawarata, zan bada saboda amfanin Najeriya.” “Duk abinda nayi a rayuwata…saboda na zama shugaban kasa ne karkashin PDP, PDP zata cigaba da zama wani sashen rayuwata.

Tun ranar da na yaga katin PDP na, a ranar nayi hannun riga da PDP. “A ranar nayi alwashin ba zan sake zama mamban wata jam’iyya ba. Zan cigaba da kasancewa dattijo mai son cigaban kasa.”

Shugaban PDP, Ayu, ya bayyanawa Obasanjo cewa: “Idan ka bar PDP, jinin PDP ba zai taba barinka ba.” Ayu ya jinjinawa Obasanjo bisa son cigaban da yake wa Najeriya inda yace yanzu kasar ta rasa irin shugabannin da take bukata.

Labarai Makamanta