Naɗin Kayode: Mutane 3 Sun Ajiye Sarauta A Masarautar Shinkafi

Kamar yadda kuka sani a kwanan nan masarautar Shinkafi ta baiwa tsohon ministan jigare Femi Fani Kayode sarautar Sadaukin Shinkafi, wanda hakan ya jawo suka daga ciki da wajen jihar Zamfara.

A safiyar yau wasu mutun uku sun ajiye sarautar su

Wadanda suka ajiye sarautar sun hada da Honarabul Bilyaminu Yusuf (Sardaunan Tsafe)

(2)Alh. Umar Bala Ajiya (Dan Majen Shinkafi)

(3) Hajiya Hadiza Abdul’azeez Yari (Iyar Shinkafi)

Sun ce sun ajiye sarautar su ne saboda abunda ke faruwa a masarautar Shinkafi, bai kamata a ce an baiwa Fani Kayode sarauta ba saboda siyasa, kamata ya yi duk wanda za a baiwa sarautar gargajiya ya kasance ya kawo wani cigaba ga masarauta, ko cigaba ga yanki, ko cigaban tattalin arziki, ko samar da tsaro, ba wai a rinka bayar da sarauta saboda siyasa ba.

A bisa wadannan dalilai suka ajiye sarautar su, sannan suna godiya a bisa sarautun da aka ba su, wacce a yanzu sun ajiye ta.

Labarai Makamanta