Mutuwar Tafa Balogun Babban Rashi Ne A Kasa – Fadar Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa a jiya ne shugaba Buhari ya mika gaisuwar ta’aziyyar sa ga rundunar yan sandan Najeriya, yan uwa da abokan arziki na tsohon sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Tafa Balogun da ya rasu a ranar Alhamis.

Shima dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, Sufeto Janar Usman Baba da gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola sun mika na su sakon ta’aziyar.

Tsohon Babban Sufeton ‘Yan-sandan Nijeriya, Mustapha Balogun, wanda aka fi sani da Tafa Balogun ya rasu bayan wata gajeruwar jinya a Lagos, yana da shekara 74.

Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Mista Femi Adesina ya sanar da sakon. Buhari, ya tuna yadda Balogun, a lokacin da yake rike da mukamin IG, ya yi iyakacin kokarin sa wajen ganin ‘yan sanda sun yi aikin su yadda ya dace a karkashin tsarin dimokradiyya.

Sannan kuma kwazonsa ya kara kwarin guiwa ga jami’an a cikin Rundunar wadanda suka yi aiki karkashinsa. Buhari ya ce tunanin sa yana tare da iyalai, gwamnati da jama’ar jihar Osun, da kuma tsoffin abokan aikin Tafa Bolagun bisa rashin shi da suka yi.

Labarai Makamanta