Mutuwar Attahiru Za Ta Mayar Da Hannun Agogo Baya A Fuskar Tsaro

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya kwatanta rasuwar babban hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a matsayin wani abu da zai haifar da koma baya ga kasar.

Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a sa’o’i bayan rasuwarsa.

Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgi da ya auku a kusa da filin tashin jirage da ke Kaduna a arewa maso yammacin kasar.

Jirgin ya taso ne daga Abuja zuwa Kaduna a cewar wata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta fitar.

“Hadarin jirgin, ya yi mana kwaf daya a makasa, a kuma daidai lokacin da dakarunmu suka samo bakin zaren kawo karshen matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta.” Buhari ya ce a sanarwa ta Shehu wacce ya wallafa a shafin Twitter.

Buhari wanda ya yi addu’a ga mamatan, ya sha alwashin ba za a manta da irin saudakarwar da suka yi ba.

A daren ranar Juma’a ministan tsaron kasa Janar Bashir Salihi Magashi (rtd) ya je fadar Buhari ya yi masa karin bayanin kan hatsarin.

A watan Janairu, Buhari ya nada Janar Attahiru, wanda ya gaji Janar Tukur Buratai tare da sauran hafsoshin sojojin kasar.

Wannan shi ne karo na uku a wannan shekara da jirgin sojin Najeriya ke yin hatsari ko ya bata a neme shi a rasa.

A halin da ake ciki fadar shugaban kasar, ta fitar da sunayen mutum 11 da suka mutu a hatsarin jirgin:

  • Lt Gen. I. Attahiru
  • Brig Gen. MI Abdulkadir
  • Brig Gen. Olayinka
  • Maj. LA Hayat
  • Maj. Hamza
  • SGT Umar

Matuka Jirgin Da Masu Hidima

  • FLT LT TO Asaniyi
  • FLT LT AA Olufade
  • ACM Oyedepo

Labarai Makamanta