Rahoton dake shigo mana daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar Jam’iyyar APC a jihar ta bayyana cewa, karin rikicin gida da jam’iyyar PDP ke fuskanta alheri ne gare ta saboda hakan zai kara kaimin nasararta a zaben 2023 mai zuwa.
An ruwaito cewa, kungiyar goyon bayan Atiku a Filato mai suna Plateau for Atiku Movement (PAM) a ranar Talata ta yi taron ‘yan jarida don nuna barranta da tsohon gwamnan jihar Jonah Jang.
Kungiyar ta bayyana rashin goyon bayanta ga Jonah David Jang ne bisa zargin ya koma tsagin gwamna Nyesom Wike mai adawa da Atiku. Gwamna Wike na ci gaba da bayyana adawarsa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar tare da neman a tsige shugaban PDP na kasa Iyochia Ayu.
A taron da kungiyar ta gudanar tare da jagorancin Istifanus Mwansat ta ce, Jang ya basu kunya wajen juyawa Atiku baya tare da bin sahun Wike. Gwamna Wike dai na ci gaba da bayyana cewa, a shirye yake da ‘yan tawagarsa don su tattauna da kuma yin sulhu da shugabannin PDP.
A bangarenta, APC ta ce hakan ya yi mata dadi, inda sakataren yada labaranta Sylvanus Namang yace nan gaba kadan mambobin PDP za su samu rabuwar kai mafi muni.
A cewarsa: “Jang ne mamallakin PDP saboda tsarin komai shi ke tafiyar dashi. Saboda haka, don sun nuna rashin goyon bayansa hakan zai dagula lamari ne kawai. Ba zan ce mun ji dadin haka ba saboda muna son abokan hamayya masu karfi, amma ta wata hanyar muna jin dadi saboda samun nasara cikin sauki.”
You must log in to post a comment.