Muna Kashe Biliyan 10 Duk Wata Wajen Ciyar Da Dalibai – Minista

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya na kashe kimanin naira bilyan 10 a wata wajen shirin ciyar da daliban makarantun firamare a fadin tarayya.

Wannan aiki na gudana ne karkashin Ministar tallafi, jin kai, da jin dadin jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

Jagoran shirin, Dr Umar Bindir, ya bayyana hakan ranar Litinin, a taron masu ruwa da tsaki na kwana biyu kan samar da takardar doka kan shirin kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito.

Dr Bindir ya bayyana cewa akwai muhimmancin a samar da takardar tsari kan shirin ciyar da dalibai don a samu cigaban shirin. Yace ana ciyar da sama da dalibai milyan 10 a rana kuma N100 aka yi kiyasi kan kowani yaro a rana.

A cewarsa: “Yau muna mayar da hankali ne kan shirin ciyar da daliban makarantun firamre tare da hadin kan shirin abinci na majalisar dinkin duniya watau World Food Programme (WFP) don samar da takardar tsare-tsare.”

“Wannan zai bada dama wajen samun cigaban shirin kamar da shugaban kasa yayi umurni.” “A yanzu haka muna ciyar da kimanin dalibai milyan 10 kuma nan da makwanni da watanni zasu zama milyan 12.”

Labarai Makamanta