Muna Dab Da Shafe Tarihin Ta’addanci Da ‘Yan Ta’adda A Najeriya – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi gargadi ga maciya amanar da suke yunkurin haddasa fitina da yaki a Nijeriya da cewa za su hadu da mummunan sakamako ba tare da bata lokaci ba.

Shugaba Buhari yayi wannan furucin ne bayan ya gana da shugaban hukumar zabe (INEC) na kasa Farfesa Mahmud Yakubu kan yawaitar kona ofishin zabe da ake yi a wasu a sassan Jihohin kudancin Nijeriya.

Buhari ya ƙara da cewar ; “ina karban rahoto akan abinda yake faruwa na harin ta’addanci, masu daukar nauyin ta’addanci suna yi ne don su durkusar da wannan Gwamnatin, labarin matsalar tsaro a Nijeriya ya karade duniya, wadanda suke neman mulki ido a rufe abune a bayyane suna nema ne ta mummunar hanya, kwanannan zasu sha mamaki, mun basu lokaci isasshe”.

Wadanda suke rashin hankali a yanzu a wasu sassan Nijeriya ba su san me ya faru ba na asaran rayuka lokacin yakin basasa, mu da muke fagen yaki a wancan lokaci na yakin basasa da muka shafe tsawon watanni 30, zamuyi maganin tsagerun da suke neman haifar da yakin basasa a yanzu kamar yadda mukayi maganin wancan, daga yanzu zuwa kowane lokaci zamu kasance masu tsananta wa ga masu yunkurin haddasa yaki a Nijeriya, inji shugaba Buhari.

Buhari yaci gaba da cewa: mun canza shugabannin hafshin sojojin Nijeriya da babban Sufeta janar na ‘yan sanda, mun basu umarni da su bamu cikakken tsaro a Nijeriya.

Labarai Makamanta