Muna Dab Da Kulle Layukan Da Ba A Yi Wa Rijista Ba – Pantami

Wa’adin da hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta ɗiba domin rajistar layin waya da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN ya kusan cika.

NCC ta tunatar da ƴan Najeriya a shafinta na Twitter cewa ranar shida ga watan Mayu wa’adin da ta bayar zai cika.

Rajistar ta shafi masu amfani da layukansu sadarwa su bayar da sahihiyar lambar shaidarsu ta NIN domin haɗa ta da layinsu.

Kuma duk layin wayar da ba a yi wa rajista ba da lambar NINza a rufe shi.

Labarai Makamanta