Muna Dab Da Janye Tallafin Mai – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta kara jaddada wa yan Nijeriya cewa su shiryawa karin farashin man fetur saboda matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki.

Karamin ministan mai, Chief Timipre Sylva, shine ya bayyana haka ga manema labarai a wajen yaye dalibai da basu kyaututtuka a jami’ar Patakwal, jihar Rivers.

Sylva yace nan bada jimawa ba gwamnati zata zare tallafin man fetur, wanda a cewarsa wasu yan kasuwa ne kadai ke amfanaa da tallafin.

Labarai Makamanta