Muna Dab Da Fara Aikin Titin Dogon Kaduna Zuwa Kano – Ministan Sufuri

Yayinda aka kammala ginin layin dogon Legas zuwa Ibadan kuma ake shirin kaddamar da shi a Yuli, gwamnatin tarayya na shirin fara ginin Kaduna zuwa Kano, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana hakan ranar Juma’a.

Amaechi ya yi wannan jawabi ne yayinda ya kai ziyara wajen gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Amaechi ya bayyana cewa jihar Kano na da muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya saboda shahararta da harkar kasuwanci. A cewar Amaechi, nan zuwa watan Yuli za’a fara aikin hada Kaduna da Kano da kuma Ibadan da Abuja, hakan zai baiwa matafiya daman tafiya daga Legas zuwa Kano kai tsaye.

“Mun zo nan ne domin ganin inda aka kwana kan lamarin tashar kan tudu ta Dala saboda nan da Yuli, zamu fara aiki kan layin dogon Kano-Kaduna,” “Kuma idan muka hada Kano da Kaduna da kuma Ibadan da Abuja, zamu fara samun saukin matsalar sufurin kayayyaki.”

“Kano na da muhimmanci ga Najeriya, hakazalika Kano na da muhimmanci ga ma’aikatar jirgin kasa kuma muna kokarin kawo tashar ruwa Kano.”

Da yake mayar da martani Gwamna Ganduje ya bayyana farin cikinsa kan irin aiki da Amaechi keyi na bunƙasa ayyukan raya ƙasa.

Labarai Makamanta