Muna Dab Da Dira Arewa – Tsagerun Inyamurai

Kungiyar Mayakan Inyamurai ta IPOB, ESN ta bayyana cewa nan babda dadewa za su dira yankin Arewa.

Hakan ya biyo wani martani ne da ƙungiyar ta fitar game da wani zargi da Kungiyar Miyetti Allah za su shigo da wasu yan uwan su 5000 da taya su samar musu kariya da tsaro daga ESN dake kai musu hari.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa a wannan takarda wanda mai magana da yawun kungiyar Emmanuel Powerful ya sa wa hannu, ya ce ” Shege ka fasa, suna jiran wadanda ‘Yan kungiyar Miyetti Allah suka ce za su shigo da su yankin. Sai sun rai na kasu.

” Wannan abu cin fuska ne ga mu Inyamirai, amma kuma ina so in sanar musu cewa muna nan muna jiran su su shigo su gani. Ba jiran su ma kawai muke yi ba, ita kanta yankin Arewan su sauraremu muna nan dirowa yankin.

Yankin Kudu maso Gabas, sun kirkiro wata kungiya mai suna ESN, wanda ake zargi da bi bin rugagen fulani suna babbakewa wai su tattara su fice musu daga yanki.

Haka kuma ana zargin su da kashe yan Arewa a hare-Hare da dama a yankin.

Labarai Makamanta