Muna Da Rahotannin Sirri Na Masu Ɗaukar Nauyin ‘Yan Bindiga – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewar akwai rahotanni da bayanan sirri da take dasu dangane da masu ɗaukar nauyin ‘yan Bindiga a Najeriya musamman yankin Arewacin kasar, kuma nan gaba ba da dadewa ba za ta fallasa su.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno ya tabbatar da hakan, inda ya ce wasu mutane suna amfani da damar tabarbarewar yanayin tsaro a kasar don amfanar kansu da kansu domin cimma manufofin su na son zuciya.

Da yake magana a ranar Talata bayan taron majalisar tsaron kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta, Monguno ya ce gwamnati ba za ta lamunci lamarin ba. Ya gargadi duk wadanda ke tayar da kayar baya da su daina ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

“Tabbas, har yanzu shugaban kasa yana ci gaba da nuna damuwa game da matakin tsaro, wanda ake ganin yana neman zama mummunan aiki, kuma da yardar Allah komai zai daidaita.

“Ganin cewa muna da sabuwar kungiya tare da sabbin shugabannin hafsoshin tsaro, shugaban kasa ya bukaci dukkanmu da mu rubanya kokarinmu, musamman ganin abubuwan da suka faru makonni biyu da suka gabata,” in ji Monguno.

“Yanzu, ina bukatar in kara jaddada cewa akwai wasu mutane a kasar nan wadanda suka dauki matsayin da ya wuce abin da ya kamata su zama. “Bayanan da muke samu daga majiyarmu, bayanan da nake dasu da kuma na sauran bayanan sirri, sun nuna cewa muna da wasu kungiyoyi, na wasu mutane da suke cin gajiya saboda rashin tsaro, musamman satar mutane.”

Ya kuma gargadi wadanda ba ‘yan jiha ba da ke haifar da matsaloli a sassa daban-daban na kasar nan da su daina yin hakan, ya kara da cewa hukumomin leken asiri sun sanya musu ido, kuma za suyi maganin su.

Labarai Makamanta