Muna Ciyar Da Dalibai Milyan 9 Kullum A Najeriya – Ministar Jin Kai

Ministar jin ƙai tallafi, walwala da jin dadin al’umma, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa sama da dalibai milyan tara na amfana da shirin ciyar da daliban firamare abinci watau NHGSFP ko wace rana a faɗin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya ce Ministar ta bayyana hakan ne yayin taron mika kayan girki ga gwamnatin jihar Benue a yankin ƙaramar Hukumar Wurukum.

Sadiya, wacce ta samu wakilcin Mataimakin Dirakta Ladan Haruna, ta bayyana cewa an tsara shirin ne domin tsomo yan Najeriya daga cikin bakin talauci, da wahalar rayuwa.

Ta ce an dauki masu girki sama da 100,000 a fadin tarayya. Ministar ta baiwa al’ummar Najeriya tabbacin cewa ba za tayi kasa gwuiwa wajen tabbatar da jin dadinsu ba.

Da yake jawabi Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, wanda ya karbi bakuncin kayayyaki yace lallai kayayyakin da kudinsu ya kai Naira miliyan 400 zai taimaka matuka.

Gwamna wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin jihar, Farfesa Tony Ijohor, yace gwamnatinsa ta horar da masu girkin kan tsafta da bin dokokin COVID-19.

Labarai Makamanta