Mnistan ƴada labaru da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce kudaden da ake ware wa ma’aikatarsa sun yi kadan wanda kuma ke kawo cikas wajen ƴaki da labaran ƙarya da kuma kalaman batanci.
Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa a 2023.
Ya ce ma’aikatarsa na bukatar kudade da ya kamata domin ƴaki da labaran ƙarya da kuma kalaman batanci.
“Idan akwai ma’aikatar da ya kamata a ware wa kudade da yawa, to ita ce ma’aikatar ƴada labaru,” in ji Lai.
Ya ce duk da cewa an yi watsi da gargadin da Amurka ta bai wa ‘yan kasarta a Najeriya kan batun rashin tsaro a Abuja, amma ba a yi hakan ba yadda ya kamata na ganin hankalin ‘yan Najeriya ya kwanta.
You must log in to post a comment.