Muna Biyan Miliyoyi Kudaden Haraji Ga ‘Yan Bindiga – Jama’ar Birnin Gwari

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna na bayyana cewar a baya-bayan nan wasu ƙauyuka a yankin sun biya kimanin naira miliyan 45, a matsayin sulhu da ‘yan Bindiga.

Ƙauyukan su fiye da goma a mazaɓar Magajin Gari ta 2 sun biya kuɗaɗen ne bayan ‘yan fashin dajin da ke yankin, sun nemi lallai su biya wannan diyya, matuƙar suna son zaman lafiya.

Birnin Gwari a Kaduna, na cikin yankunan da suka fi fama da taɓarɓarewar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya.

Bayanai sun ce wani hari da ‘yan fashin daji suka kai ƙauyen Awaro kimanin mako uku a baya ne, ya ƙara tsorata mutanen yankin har suka miƙa wuya.

Sace matan aure da ƙananan yara da rana suna tsaka da halartar biki, ya sa wasu tserewa zuwa gudun hijira.

Wani shaida ya ce sun yi amfani da harin wanda aka kashe mutum ɗaya a matsayin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

Ya ce, “sun shaida mana cewa wannan somin-taɓi ne kuma su basa ma son batun sulhu, wannan dalili ya sanya mutane shiga gudun hijira. Garin da suka je suka diba mata a gidan biki na cikin manyan garuruwa”.

Shi ma wani mai tattara bayanai kan hare-haren ‘yan fashi a yankin ya faɗa wa BBC cewa ƙauyukan goma sha uku na cikin al’ummomin da suka tsallake harajin ‘yan fashi a damunar da ta wuce.

Amma kuma a baya-bayanan sun gargaɗe su da cewa ko dai su biya su zauna lafiya a yanzu, ko kuma su yi noma a damuna mai zuwa, ko kuma su ci gaba da fuskantar hare-hare.

“Sai da kowanne magidanci ya biya kudin, har da wadanda suke hijira, ko da hali ko ba hali, wasu ma ranta musu aka yi suka biya. Ƙauyuka 14 ne suka hada kudin.” Ya kuma kara da cewa an biya kudin ne a satin da ya gabata.

Shi ma wani shaida da ya ce ya ga kuɗin da idonsa, ya shaidawa BBC cewa; “Wasu na cewa miliyan 45 amma akwai yiwuwar yafi haka, a buhunan taki aka zuba kudin, akwai wadanda suka biya dubu 100 wasu kuma dubu 200”.

Rahotanni sun ce zuwa yanzu ƙauyukan da suka biya wannan haraji, ba su fuskanci wani sabon hari ba. Sai dai fargaba da zaman ɗar-ɗar sun dabaibaye zukatansu saboda rashin tabbas.

Da yawan waɗanda suka tafi gudun hijira zuwa garuruwa kamar Birnin Gwari, sun kasa komawa gidajensu a jihar ta Kaduna. Wadda mahukunta ke cewa ayyukan ‘yan fashin daji sun ƙaru a shekarar da ta wuce.

Labarai Makamanta