Muna Binciken Gaskiyar Labarin Mutuwar Shekau – Rundunar Soji

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar soji tace har yanzun bata samu ingantaccen bayani kan rahoton mutuwar shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Sheƙau ba.

Wani rahoton bincike ya bayyana cewa Sheƙau ya mutu ne a wata fafatawa da suka yi da mayaƙan dake fafutukar kafa kasar musulunci a nahiyar Afirca (ISWAP).

Rahoton ya bayyana cewa, Abubakar Shekau yaji mummunan rauni yayin da yayi ƙoƙarin kashe kansa don kada abokan hamayyarsa ISWAP su kama shi a wata fafatawa da suka yi da talatainin daren ranar Laraba.

Wani Rahoton ya kuma bayyana cewa shugaban Boko Haram ɗin ya sheƙa lahira bayan jiwa kansa mummunan rauni, sakamakon harbin kanshi da kanshi da ya yi da Bindiga.

A wata tattaunawa da aka yi da ƙwararre a ɓangaren tsaro, Kabiru Adamu, yace ko an kashe shakau ko yana raye, ISWAP na ƙara ƙarfi idan ka duba irin ayyukan da suke yi a yanzun.

“Abinda wannan rahoton ke nuna wa rundunar soji shine sun bar ISWAP ta ƙara ƙarfi a ɓangaren kai hare-haren su, kuma wannan mummunan saƙo ne suke aikewa ƙungiyoyin ta’addanci.” “Wannan saƙon na nuna wa mutanen dake shiga rundunar soji da waɗannan ƙungiyoyi cewa gara su shiga waɗannan ƙungiyoyin na ta’addanci saboda sunfi rundunar soji ƙarfi.

Da aka tuntuɓi daraktan yaɗa labarai na rundunar, Brig.-Gen. Bernard Onyeuko, ya faɗawa manema labarai ta hanyar tura saƙo cewa bashi da bayani akan rahoton. “Kuyi hakuri, bani da bayani akan haka.” inji shi.

Labarai Makamanta