Mun Yi Tir Da Walimar Da Ganduje Ya Shirya Wa Tinubu – Ƙungiyoyin Arewa

Gamayyar kungiyoyin cigaban arewacin Najeriya sun yi Allah wadai da matakin da Gwamnan jihar Kano Ganduje ya ɗauka na karrama Tinubu a fadar gwamnatin jihar da bikin zagayowar ranar haihuwar shi.

Gamayyar kungiyoyin sun bayyana wannan mataki na Ganduje a matsayin abin takaici domin ko a jihar Legas inda Tinubun ya taɓa yin Gwamna ba a taɓa gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar shi a gidan Gwamnati ba, to a bisa wane dalili za a yi hakan a Kano.

Gamayyar kungiyoyin sun bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da suka fitar wacce ta samu sanya hannun Kodinetan Ƙungiyar na jihar Kano Ali Ahmed kuma aka rarraba ta ga manema labarai.

“Muna kira da babbar murya ga Gwamnan Ganduje da ya yi fatali da wannan shiri nashi na yunƙurin zubar da kima da darajar gidan gwamnatin Kano saboda dalilan son zuciya na siyasa, domin tabbas abu ne wanda ba za’a lamunta ba”.

Gamayyar kungiyoyin sun cigaba da cewar abin damuwa ne matuƙa a jiha kamar Kano wadda ta samar da manyan Mutane a tarihin Najeriya amma ba’a taɓa samu lokacin da aka gudanar da bikin zagayowar haihuwar wani a fadar gwamnati ba, sai a yanzu ne za’a dauko wani bakon haure wanda ba ɗan jiha ba, kuma bai taɓa tsinanawa Jihar komai ba ace za’a yi mishi wannan karramawa lallai hakan cin fuska ne ga Kanawa.

“Ko kaɗan Tinubu bai cancanci wannan karramawa da Ganduje ke kokarin yi ba, duba da irin halin ko in kula da ya nuna akan kisan Hausawa da ‘yan uwanshi Yarbawa suka riƙa yi, Tinubu bai ziyarci al’ummar Arewa ya jajanta musu ba, sannan bai fito ya yi Allah wadai da hakan ba, to babu dalil na karrama shi a yankin Arewa ballantana jihar Kano jigo a Jihohin Arewa”.

Daga karshe gamayyar kungiyoyin Arewan sun yi tir da matakin gwamna Ganduje na karrama Tinubu, sannan sun bayyana rashin lamuntar su da hakan, sannan za suyi dukkanin mai yiwuwa na faɗin cas ga dukkanin wani da zai ce wa yankin arewa kule!.

Labarai Makamanta