Ministan harkokin jiragen sama, Hadi Sirika yana ganin cewa babu wanda ya isa ya bige jam’iyyar APC mai mulki a babban zabe mai zuwa a jihar Katsina Mahaifar Shugaban ƙasa Buhari kuma Jihar da ya shi ya fito.
A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta a kwanan nan, an ji yadda Sanata Hadi Sirika yake cika baki da cewa APC ta tanadi kudin yakin zabe, kuma za ta yi amfani dasu wajen cin zaɓe.
Hadi Sirika ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin da aka shirya domin tarawa ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyya mai mulki ta APC Dr. Umar Dikko Radda kudin kamfe.
An shirya taron na musamman ne a birnin tarayya Abuja da nufin karbar gudumuwar magoya baya wajen yakin neman zaben Dikko/Jobe a jihar Katsina.
Da ya tashi jawabi, Sirika wanda Minista ne a gwamnatin Muhammadu Buhari tun a shekarar 2015, yace ba za ta yiwu ‘yan adawa suyi galaba a kansu ba, za su yi dukkanin mai yiwuwa wajen samun nasarar lashe zabe a jihar Katsina.
*Ai ranar zaben tana zuwa. Saboda haka za mu tara kudi, kuma za mu tara kayan masarufi, kuma muna da su. Kudin ba? Wallahi muna da su, Wallahil Azim muna da su. Muna da kayan aiki (kudi) kuma na fadi, muna da su.”
You must log in to post a comment.