Ministar Samar da Agaji da Jinkai, Sadiya Farouq ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta tallafawa ‘yan gudun hijira 5,576 dake zama a sansanin ‘yan gudun hijira dake Wasa a Abuja.
Sadiya ta ce gwamnati ta yi haka a wannan lokaci da duniya ke tunawa da ranar bada da Agaji da Jinkai sannan da cika shekara daya da kafa ma’aikatar samar da Agaji da jinkai a Najeriya.
Minista ta kara da cewa gwamnati ta raba kayan abincin da suka hada da buhuna 80 na shinkafa, buhuna 15 na wake, jarkoki 25 na mangyada, bargo 500, Katan 22 na Madara da turaman zannuwa 100.
Kodinatan sansanin Jeoffery Bitrus ya mika godiyarsa a madadin mazauna wannan sansani ga minista bisa wannan tallafi da suka samu.
Bitrus ya yi karin haske da yin kira ga gwamnati da ta gina asibiti a sansanin domin domin kiwon lafiyar mazauna wannan wuri.
Shugaban kungiyar mata na wannan sansanin Hafsat Ahmad ta roki gwamnati ta samar musu da wata hanya da za su rika koyan sana’a domin su iya rike kan su suma.
You must log in to post a comment.