Mun Shirya Tsaf Domin Maka El Rufa’i Kotu – Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama

Wakilin kungiyar Kare hakkin ‘dan Adam (Amnesty)reshen jihar kaduna, Alhaji Musa Jika ya bayyana cewa a shirye suke su maka Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad Elrufai muddin bai biya Korarrun Sakatarorin din din da sauran Ma’ikatan da aka sallama ba bisa ka’ida ba a fadin jihar kaduna.

“Alhaji Musa ya bayyana hakan ne yayin zantawa da Wakilinmu inda yace babu inda Dokar ‘Kasa ta bayyana cewar wani gwamna yana da karfin ikon ragewa Ma’ikatan gwamnati da aka sallama aiki kudaden sallama aikin su (Fansho).

” Yace a binciken da muka yi, mun gano cewar mafi yawancin Ma’ikatan da aka kora lokutan ajiye aikin su baiyi ba, wasu suna da sauran shekaru biyu ko uku amman duk da haka Elrufai ba tare da kirkirar wata doka ba kawai yayi gaban kansa ya sallame su. Sannnan bayan sallamar su aiki yanzu an zabtare masu Kashi 2 cikin 3 na Hakkokin su.

“Mun tattaro bayanan mu Kuma a shirye muke mu kalubalance gwamna Nasir Ahmad Elrufai har gaban kuliya muddin baiyi abinda dokan kasa ya shinfida ba. Muna da sunayen dukkan Ma’ikatan da gwamnatin jihar kaduna ta sallama ba akan tsari ba da kuma kudaden da aka ba wasu daga cikin su.

Daga karshe yayi Kira na musamman ga ‘Yan majalisar jihohin jihar kaduna da su dawo cikin hayyacin su, su sani cewa su wakilai ne na al’umma bawai na gwamna ba. Muna kallon yadda suke tafiyar da ayyukan su wanda hakan ya Sha ban ban da tsarin da mulkin dimokaradiyya ya tanada.

Related posts