Mun Rufe Layukan Waya Sama Da Miliyan 63 A Najeriya – Hukumar Sadarwa

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jumillar layin waya miliyan 63.97 aka toshe cikin shekara ɗaya a Najeriya yayin da hukumar sadarwa ta NCC ke ci gaba da haɗa lambar ɗan ƙasa NIN da layukan salula.

Wasu bayanai da NCC ta wallafa sun nuna cewa jumillar adadin layukan salula da ke aiki a Najeriya sun ragu da kashi 21.79 cikin 100 zuwa 229,582,206 a watan Oktoban 2021 daga 293,554,598 a Oktoban 2020.

A tsakanin lokacin da ake magana, adadin layukan da ke aiki ya fi yawa a watan Agustan 2021 (328,114,538) sannan ya fi raguwa a Satumban 2021 (229,467,077).

Labarai Makamanta