Mun Kwato Fiye Da Dala Biliyan Guda Daga Barayin Gwamnati – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta ce ta gano tare da ƙwato dala biliyan ɗaya da aka sace sakamakon bincikar kuɗin sata da gwamnatin ke yi tun farkon hawansa zuwa yau.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan kammala taron majalisar zartarwar ƙasar da ake gudanarwa mako-mako, wanda shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Malami ya tabbatar da cewa ƙudin da aka ƙwato an zuba su a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ƙasar cikin har da shiri gwamnati ƙasar na yaƙi da talauci.

Haka kuma ministan ya bayyana damuwar gwamnati kan cushe a kasafin ƙudin ƙasar, ya ce hakan abin takaici ne, ya kuma ƙara da cewa za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki domin magance hakan

Labarai Makamanta