Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin tarayya ta ce ta yi nasarar ƙwato dukiyar ƙasar da wasu jami’an gwamnati suka sace a kuɗaɗen ƙasar waje da suka ƙunshi fan miliyan 6.3 da yuro miliyan 5.4 da dala 390,000.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ce ana amfani da wasu daga cikin kuɗaɗen wajen aiwatar da wasu ayyuka kamar ginin hanyar Abuja zuwa Kano, da Legas zuwa Ibadan, da kuma ginin gadar Second Niger Bridge a yankin kudu maso gabas.
Ministan ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin taron bayyana ayyukan gwamnatinsu ta APC tun daga 2015 zuwa yanzu.
Kazalika, ya ce gwamnatin ta Muhammadu Buhari ta samu naira biiliyan 1.8 a cikin gida sakamakon sayar da kadarorin da aka ƙwace daga hannun wasu mutane daga 2015 zuwa 2022.
You must log in to post a comment.