Mun Kusan Kawo Karshen Mashaya A Najeriya – Marwa

Shugaban hukumar NDLEA mai yaƙi da fatauci da shan miyagun ƙwayoyi na ƙasa Buba Marwa, ya ce ana daf da kawo karshen matsalolin safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

Buba Marwa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya na NAN cewa da tallafin gwamnatin Najeriya da manyan masu ruwa da tsaki, Najeriya za ta yi nasara kan fataucin miyagun ƙwayoyi.

Ya bayyana matsalar miyagun ƙwayoyi a Najeriya a matsayin wata annoba, sai dai ya ce hukumarsa na yin dukkan mai yiwuwa don ganin an magance matsalar kuma suna samun goyon bayan da ya dace gwamnatin tarayya.

Buba Marwa ya ce hukumar na shirin shiga ƙananan hukumomi don wayar da kan mutane.

Labarai Makamanta