Mun Kashe Biliyan Uku Wajen Ciyarwa Da Azumi – Matawalle

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta kashe zunzurutun kudi har naira biliyan 2.9 wajen sayan kayayyakin masarufi domin ciyar da marasa karfi a lokacin azumi.

Wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labaran jihar Alhaji Ibrahim Dosara ya fitar ta ce motar abinci 450 gwamnati ta saye domin raba wa mutane da suka ƙunshi ƴan gudun hijira da ma’aikata da sauran mabuƙata a jihar.

Duk shekara gwamnati ta saba ware kuɗi domin rabon kayan azumi ga al’umma, duk da wasu na ganin mutane kalilan ne ke amfana da tallafin.

Kayan abincin da gwamnatin ta ce ta saya sun haɗa buhun shinkafa 60,000 da gero buhu 50,000 da masara buhu 50,000 da wake buhu 30,000 da sikari jika 10,000 da kuma tufafi shadda da atamfa 40,000.

Labarai Makamanta