Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mataimakiyar gwamnan CBN, Aisha Ahmed, ta bayyana cewa kudin da aka kashe kan buga sabbin kudi a shekara ya karu zuwa Naira Biliyan Goma N10bn.
Aisha ta bayyana hakan ne ranar Juma’a yayinda da ta bayyana gaban majalisar wakilan tarayya a madadin gwamnan bankin, Godwin Emefiele.
bayyana cewa kashi 90% na kudin da ake kashewa kan manajin Naira buga sabbin takardun kudi ake da su, babban bankin na kashe N150bn wajen buga sabbin kudi da lalata tsaffi a shekara.
Hakazalika tsohon mataimakin gwamnan CBN, Dr Kingsley Moghalu, shima ya ce lallai ana kashe kimanin N150bn a shekara. Ya ce ana amfani da kudin ne wajen buga sabbi, ajiyansu, tafiyar da su, kare su da kuma lalata tsaffi.
Bisa jawabin Aisha Ahmed, bankin ya kashe N800bn tsakanin 2017 da 2021 wajen kula da Naira. Tace: “An yi binciken cewa kudin da aka kashe wajen kula da Naira daga 2017 zuwa 2021 ya karu da N10bn a shekara kuma kashi 90% na wannan kudi buga sabbin takardun Naira ake da su.”
“Wannan na illata ayyukan CBN.” Aisha Ahmad ta ce daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta shine yadda ake buga jabun takardun Naira a jihohi, har da birnin tarayya Abuja. Ta kara da cewa hakan na illata yan kasuwa da kuma tattalin arzikin kasan ga baki daya.
You must log in to post a comment.