Mun Karbo Naira Biliyan 30 A Hannun Dakataccen Akanta Janar

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ya ce zuwa yanzu an karbe N30bn daga hannun Idris Ahmed tsohon Akanta Janar na ƙasa.

Wadannan biliyoyi su na cikin N109bn da ake zargin Idris Ahmed ya karkatar a lokacin yana rike da ofishin Akanta Janar na kasa.

Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa ya shaidawa Duniya wannan a lokacin da ya halarci wani taro da aka yi da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Kwamitin harkokin yada labarai na fadar shugaban kasa ya shirya wannan zama a Aso Villa a Abuja kamar yadda aka saba lokaci bayan lokaci.

An karbe biliyoyi a shekarar 2022 Kamar yadda Abdulrasheed Bawa ya yi bayani, daga watan Junairu zuwa Disamban 2022, sun karbe N134,33,759,574.25, $121,769,076.30, da ÂŁ21,020.00.

Wannan bayanin yana shafin EFCC da ke Twitter. Bawa ya ce sun daure mutane fiye da 3, 615 a shekarar nan, wanda hakan ya nuna da gaske ake yi wajen yakar masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annuti.

Labarai Makamanta