Mun Kammala Tattaunawa Da ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Daliban Jami’ar Greenfield – Gumi

Mashahurin Malamin addinin Musulunci wanda ya yi fice wajen sulhu da ‘yan bindiga Sheikh Dr Ahmad Gumi ya ce yan bindigan da sukayi garkuwa da daliban jami’ar Greenfield a Kaduna sun fasa kashesu kamar yadda sukayi barazana ranar Litinin.

Idan jama’a basu manta ba cewa a ranar Litnin, shugaban yan bindigan mai suna Ɓaleri Jalingo ya yi Barazanar cewa idan ba’a biya fansar Naira Miliyan 100 ba zasu kashe daliban ranar Talata.

Amma a ranar Alhamis yayin karban bakuncin iyayen daliban Afaka da aka ceto, Malamin addinin ya ce yanzu haka suna tattaunawa don ceto daliban jami’ar Greenfield.

Ya ce samun nasarar ceto daliban Afaka ya kara musu karfin gwiwa wajen tattaunawa da yan bindigan, waɗanda suka sace daliban jami’ar Greenfield wata jami’a mai zaman kanta a Kaduna.

“Har yanzu muna tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da daliban jami’ar Greenfield. Ka san sun yi barazanar kashesu gaba daya a wata rana amma bayan maganar da mukayi musu, sun sauko daga wannan ra’ayi,” yace.

“Saboda muna godiya sun fasa kisan. Kuma muna tattaunawa da su.”

Ya kara da cewa yan bindigan na kai wadannan hare-hare ne don bakantawa gwamnati rai, sannan suna hakan ta hanyar kai hari makarantun gwamnati da sace dalibai.

Labarai Makamanta