Mun Gamsu Da Rawar Da Amurka Ke Takawa Na Yakar Ta’addanci A Najeriya – Buhari

Mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa Amurka bisa rawar da take takawa wurin yaki da ta’addanci a kasarsa.

Shugaban ya fadi haka ne yayin karbar bakunci sakataren harkokin wajen Amurkar Antony Blinken, wanda ke gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki uku a Abuja.

Sanarwar wadda mai bai wa Shugaban shawara kan yada labarai Femi Adesina ya fitar ta ce “shugaba Buhari na gode wa Amurka da bai wa Najeriya damar mallakar makamai don yakar ta’addanci, da kuma horon da take bai wa sojojinta na sanin dabarun yaki.”

Kan batun cire Najeriya daga jerin kasashen da ke hana yancin gudanar da addini, shugaba Buhari ya jinjina wa Amurka, inda ya ce kasarsa na bai wa kowa damar gudanar da addinin da yake so ba tare da tsangwama ba.

A nasa bangaren Mr Blinken ya jinjina wa Shugaban Najeriyar kan alkawarin ba da gagarumar gudummawa wurin yakar matsalar dumamar yanayi, a lokacin taron sauyin yanayi da aka yi na COP26 a birnin Glasgow na Scotland.

Ya kuma ce kan sha’anin tsaro, kasashen biyu za su kara hada hannu don ganin sun gudu tare sun tsira tare.

Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurkar zai shafe kwanaki uku a Najeriya.

Labarai Makamanta