Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Najeriya – Hukumar Tsaro

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jami’an tsaro sun daƙile wani yunƙurin kai hari a Jihar Kano “wanda ka iya zama mafi muni” a tarihin ƙasar, a cewar Babban Hafsan Tsaro na Janar Lucky Irabor.

Janar Irabor ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da ya bayyana cikin wani shiri kan Ranar Dimokuraɗiyya a kafar talabijin ta Channels TV.

Ya ce an daƙile harin ne a Kano cikin makon da aka kai hari kan wani coci a garin Owo na Jihar Ondo, wanda ‘yan bindiga suka buɗe wa masu ibada wuta tare da kashe mutum fiye da 40.

“Babu mamaki ba ku da labari cewa a makon da ya wuce kaɗai da aka kai harin coci a Owo, a Kano misali, mun yi nasarar daƙile harin da ka iya zama mafi muni a ƙasar nan tamu saboda bayanan sirri da muka samu,” in ji shi.

“A wannan aikin, mun gano kayayyakin da ake haɗa abubuwan fashewa da su. Mun ƙwace ƙunshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke ƙoƙarin yin amfani da su a sassan ƙasa, har da Abuja.”

Janar ɗin ya ƙara da cewa harin Owo da aka kai ba ya nuna cewa ba a samun ci gaba a faɗin Najeriya ba, yana mai cewa “harkokin tsaro sun inganta a shekara ɗaya da ta wuce”.

Labarai Makamanta