Babban bankin kasa CBN ya yi watsi da rahotannin cewa ana samun karancin sabbin tsabar kudi a fadin bankunan Najeriya, Bankin ya ce akwai isassun kudi a bankuna a fadin kasa kuma yana kan bakan sa na daina amfani da tsaffin takardun dake yawo hannun mutane ranar 31 ga Junairu, 2023.
Bankin ya kara da cewa shi bai hana bankuna baiwa mutane sabbin kudi a kan kanta ba kawai dai an umurci bankunan ne su kara adadin kudaden da suke zubawa a na’urar ATM saboda sabbin takardun suyi yawa hannun jama’a.
Bankin yace daga yanzu sabbin kudade kadai bankuna zasu rika zubawa a na’urorinsu na ATM dake fadin kasa. Diraktan yada labaran bankin, Mr Osita Nwanisobi, ya bayyana cewa bankin ya yi wasu shirye-shirye na tabbatar da yaduwar kudaden a cikin gari.
“Ko kadan ba ce a daina bada kudi a bakin ‘kanta’ ba.” “Mun zanna da bankunan kuma muka yi ittifakin cewa a fara sanya sabbin kudaden cikin ATM saboda mutane su samu kuma ya yadu.” “Lallai wannan umurni ne. mun yi zaman ne saboda mutane na korafin cewa ba su ganin sabbin kudaden. Kuma hakan bai nufin bankuna ba zasu iya bada kudi a ‘kanta’ ba.”
“Muna da isassun kudade, kuma za’a iya amfani da tsaffin kudi har zuwa ranar 31 ga Junairu.”
You must log in to post a comment.