Mun Bankado Shirin Tayar Da Fitina A Ranar Rantsar Da Tinubu – DSS

Hukumar tsaro ta ƴan sandan ciki ta ƙasa DSS ta bayyana cewa akwai wasu da suke shirin tayar da zaune tsaye a lokacin bukukuwan mika mulki da za a yi a wasu jihohin kasar.

A wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, hukumar ta ce mutanen suna son yi wa aikin jami’an tsaro nakasu ne tare kuma da tayar da hankalin jama’a su jefa tsoro ga ‘yan kasar a lokacin.

A sanarwar wadda kakakinta, Peter Afunanya ya fitar, hukumar ta bukaci jama’a da ƴan jarida da ƴan kungiyoyin farar hula da duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar da su bi ka’idojin da aka tsara a lokacin bikin a ko’ina a fadin kasar.

Haka kuma sanarwar ta shawarci jama’a da su yi watsi da labaran karya ko na kanzon-kurege da na zuzuta al’amura da kuma duk wani abu na neman razanarwa.

Hukumar ta kuma shawarci duk wani mutum da ba shi da takardar izini ko ta tantancewa da ya kauce wa shiga wasu wuraren a lokacin da ake bikin.

DSSn ta bai wa jama’a tabbacin ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ganin bukukuwan sun wakana lami lafiya cikin nasara a ko’ina a fadin kasar.

A ranar Litinin 29 ga watan nan na Mayu 2023 ne za a yi bikin mika mulki da rantsar da sabon shugaban kasa a Abuja da kuma gwamnoni a wasu jihohin Najeriyar

Labarai Makamanta