Mun Bankaɗo Maƙarƙashiyar Juyin Mulki – Fadar Shugaban Kasa

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa sun gano wani shiri da wasu Malaman addini da tsoffin ‘yan siyasa keyi na kokarin hada baki da wasu baƙin haure wajen yiwa gwamnatin Buhari juyin mulki.

Fadar shugaban kasan ta ce an samu hujjoji kan shirin da ake yi na hada baki da wasu shugabannin kabilu da yan siyasa wajen alanta rashin imaninsu da shugaba Buhari.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Talata. “Wani shiri da wasu Malaman addini da tsoffin shugabanni ke yi, ana niyyar jefa kasar cikin rudani da rikici, wanda hakan zai tilasta yin juyin mulki,”.

“Wasu karin hujjoji sun bayyana cewa wadannan mutanen yanzu haka na kokarin shawo kan shugabannin wasu kabilu da ‘yan siyasa a fadin tarayya, da niyyar shirya wani taro inda za’a nuna rashin amincewa da shugaban kasa, wanda hakan zai jefa kasar cikin rikici.”

Labarai Makamanta