Mulkin Najeriya Na Hannun Baragurbi Ne A Yanzu – Na’Abba

Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Alhaji Ghali Umar Na’Abba, ya bayyana cewa Najeriya ta shiga wata sarkakiya a tarihi a yanzu, wanda hakan ke tabbatar da cewar babu shugabanci a Najeriya.

Ghali ya koka ne a kan yawaitar kashe-kashe da tashe-tashen hankula a ƙasar nan, tare da cewa talakawa na ɗanɗana kuɗar sakacin da gwamnati ta yi ana ta tashe-tashen hankula, ba tare da ɗaukar wani mataki mai muhimmanci daga gwamnati ba.

Kalaman Ghali wani shagube ne kan yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa tsayar da kashe-kashen da ke faruwa a faɗin ƙasar nan, inda ya bar Jaki ya koma dukan taiki.

“Baragurbi mafi lalacewa a cikin mu ne aka ɗauki amanar jagorancin al’ummar ƙasar nan aka damƙa a hannun sa.”

Ya yi waɗannan kausasan kalaman ne a wani taron da ya haɗa ƙabilun Najeriya daban-daban a Abuja, a ranar Litinin.

Ghali ya yi kalaman ne a lokacin da Buhari ya cika shekaru shida a kan mulki, ba tare da magance matsalar tsaro da ya rika kamfen zai magance ba idan ya hau mulki.

Kawar da matsalar tsaro na daga cikin manyan alkawuran da Buhari ya dauka tun kafin ya hau mulki.

Yan Najeriya musamman ‘yan Arewa sun yi goguwar Buhari ne a 2015 domin ya magance matsalar tsaro da yankin ke fama da ita a wancan lokaci wanda ita ce matsalar hare-haren Boko Haram.

Sai dai kuma shekaru shida bayan haka, maimakon a samu sauki, matsalar tsaro tsanani ya kara yi musamman a yanzu kuma a yankin Arewa Maso Yamma da Kudancin Najeria.

Labarai Makamanta