Mulkin Buhari Zai Tarwatsa Najeriya – Tsohuwar Ministar Ilimi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohuwar ministan ilimi, Oby Ezekwesili, ta maida martani ga hukumar tsaro DSS kan cewa masu sukar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na shirin tarwatsa Najeriya.

A cewar tsohuwar ministar, babu wanda ke son tarwatsa Najeriya face salon mulkin shugaba Buhari da halin ko inkula da yake nunawa, shine babban abinda zai tawatsa Najeriya.

Ozekwesili ta bayyana haka ne a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Lahadi hukumar DSS ta bayyana masu sukar shugaba Buhari da marasa ɗa’a Kuma ta zargesu da barazana ga zaman Najeriya tsintsiya ɗaya.

Wasu yan Najeriya na ganin gazawar shugaba Buhari wajen shawo kan lamarin tsaron ƙasar nan, musamman wajen magance yan ta’addan Boko Haram, Satar mutane, da kuma yan bindiga a faɗin ƙasar.

“Muna Allah wadai da kalaman wasu mutane marasa ɗa’a waɗanda ke cigaba da zama barazana ga gwamnati da kuma kasancewar Najeriya ɗaya.” Inji Hukumar DSS.

Yayin da take martani kan wannan kalaman na hukumar DSS a shafinta na kafar sada zumunta Tuwita, Oby Ezekwesili, ta ce: “Kamata yayi DSS ta tura wannan kalaman nata kai tsaye ga shugaba Buhari, wanda shine mai kula dasu.”

“Babu wani mutum ɗaya a Najeriya dake son jefa ƙasar cikin matsaloli ko barazanar kasancewar ƙasar tsintsiya ɗaya sama da shugaban ƙasa, wanda ayyukansa, da rashin kulawarsa ke ƙara barazana ga kasancewar Najeriya ɗaya. “Saboda haka ina rokon ku DSS ku tuhumi shugaban ku amma ba wasu yan Najeriya ba.”

Labarai Makamanta