Mulkin Buhari Ya Wahalar Da Talaka – Sarkin Yakin Buhari

Gwamnatin shugaba Buhari ya kamata ta sauya salon tafiyar da mulkin ta, saboda ba a taba gwamnatin da talaka ke kukan yunwa da talauci irin wannan Gwamnatin ba.

Yunwa na kashe bayin Allah ga rashin tsaro ya yi kamari. Baya ga kulle bodojin Arewa da aka yi don gudun shigowa da makamai duk a banza.

Gwara gwamnati ta bude mana bodojin mu ko ma sami saukin radadin talauci da yunwa a Arewa. Don talauci da yunwa ne kadai zai iya harzuka talaka bore ga gwamnati.

Mashawartan Buhari ba sa ba shi shawara ta gaskiya.

Daga Abdul Ra’uf Matawalle

(Sarkin Yakin Buhari)

Related posts