Ƙungiyar Kare Muradun Fulani Makiyaya ta Najeriya (MACBAN), ta bayyana cewa ɗaukacin Fulani sun mara wa Buhari baya ya ci zaɓe, amma sun yi wahalar banza, domin babu abin da gwamnatin ta tsinana masu.
Shugaban MACBAN na Ƙasa, Bala Ngelzarma ne ya bayyana haka, yayin wani taron daya kira na ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce sun yi zaton gwamnatin Buhari za ta share masu hawaye amma maimakon haka, sai ma tsangwama, naƙasu, tasku da kuma watsi da su da gwamnatin ta yi.
“Gwamantin Buhari ta kashe fiye da naira bilyan 500 a fannin noma, amma ta wofintar da fannin kiwo, wanda ba a kashe masa komai ba.
“Duk wanda ke shakku ko tababa ya je ya duba kasafin kuɗin jihohi da na tarayya, zai ga cewa fannin kiwo bai amfana da komai ba.
“Hatta Shirin Zamanantar da Kiwon Dabbobi da ake ta zugugutawa, babu wani tasiri da zai yi idan ma har shirin ya tabbata an aiwatar da shi a wasu jihohi. Misali, ta yaya za a ce a Jihar Adamawa wai za a gina cibiyar kiwon dabbobi ta zamani, wadda za ta iya ɗaukar shanu 20,000, alhali a jihar akwai shanu fiye da miliyan biyu?”
Ngelzarma ya ce mulkin Buhari ya janyo wa fulani tsangwama saboda masu adawa da Buhari su na haɗawa da fulani da Buharin duk su tsane su.
You must log in to post a comment.