Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya bayyana cewa bai taba ganin mulki irin wannan na jam’iyyar APC ba .
A cewarsa mafi muni a cikin mulkin soja da Najeriya ta yi fama da shi a tarihi, ya fi gwamnatin shugaba Buhari sauki ga yan Najeriya.
Yace babu makawa jam’iyyarsa ta PDP zata karbi mulki a babban zaɓen 2023 saboda gazawar APC ta kowane ɓangare .
Gwamnan jihar Benuwai Samuel Ortom, ya sake sukar gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Ortom ya yi ikirarin cewa duk lalacewar gwamnatin sojoji ta fi mulkin yanzu ƙarƙashin jam’iyyar APC sauki da jin daɗi.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da yake masa tambayoyin manema labarai a Makurɗi, jim kaɗan bayan dawowarsa daga ganganmin PDP na ƙasa.
You must log in to post a comment.