Mr LA Ya Sha Kaye A Zaben Fidda Gwanin PDP Na Sanatan Kaduna Ta Tsakiya

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Ibrahim Usman, ya lashe zaben fidda gwani na ɗan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya karkashin inuwar jam’iyyar PDP, inda ya doke Lawal Adamu (Mr LA) wanda a baya aka ayyana matsayin wanda ya yi nasara.

Usman Ibrahim wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa, ya tashi da ƙuri’u 210 daga cikin 223 da aka kaɗa wanda ya bashi damar lallasa abokan fafatawarsa 5.

Babbar Kotun tarayya dake zama a Kaduna ta rushe zaɓen fidda gwanin farko da PDP ta shirya a mazaɓar Sanatan Kaduna ta tsakiya ranar 24 ga watan Mayu inda ta bada umarnin sake gudanar da sabon zaɓe.

Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Muhammad Umar ta rushe zaɓen farkon ne saboda saba wa doka da aringizon kuri’u kana ta umarci PDP ta sake sabon zaɓe cikin kwanaki 14.

Alƙalin ya yanke hukunci ne biyo bayan ƙarar da ɗaya ɗaga cikin ‘yan takara, Ibrahim Usman ya kai gabansa, yana kalubalantar zaɓen farko wanda aka ayyana Lawal Adamu a matsayin wanda ya samu nasara.

Bayan kammala sabon zaɓen wanda ya gudana ranar Litinin, shugaban kwamitin shirya zaɓen, Istifanus Mwansat, ya ayyana Ibrahim Usman a matsayin wanda ya zama zakara. Yace Usman ya samu kuri’u 210 daga cikin kuri’un Deleget 223 da aka tantance su kaɗa kuri’unsu a tsakanin yan takara.

Lawal Adamu ya samu kuri’u biyar yayin da Farfesa Usman Muhammad Ya samu kuri’u biyu.

Labarai Makamanta