Miyyeti Allah Ta Yi Kiran A Yi Gaggawar Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hure reshen jihar ta goyi bayan kiraye-kirayen ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda a Najeriya.

Da take bayyana goyan bayan matsayar Majalisar Dattawa, Wakilai da Kakakin Majalisar da suka yi wannan kiran a baya, kungiyar ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta yi duk abin da ya dace don dakile barnar ‘yan bindiga.

Shugaban Kungiyar na jihar Bauchi, Alhaji Sadik Ibrahim Ahmad, wanda ya zanta da jaridar The Nation a ranar Lahadi ya bayyana matsayin Ƙungiyar tasu akan ‘yan Bindigar.

“‘Yan ta’adda mutane ne masu kokarin lalata halaltattun ayyukan al’umma, ba su da wani amfani idan da gaske gwamnatin tarayya ta ke, ya kamata ta yi abin da ake bukata tare da samar da mafita mai dorewa kan kashe-kashen da ‘yan fashi da ake kira ‘yan bindiga ke yi.”

Dangane da batun takarar jam’iyyun siyasa gabanin zabukan 2023, ya ce a bar talakawa su zabi shugabanninsu ba tare da la’akari da kabila ba ko addini ba. A cewarsa: “Ko Bayarabe ne, Bahaushe ko Igbo, da zarar ka cancanta, ka cancanci shugabancin kasar.

“Ya kamata mutane su nemi shugabanni masu gaskiya idan muna son hada kanmu. Shugabanninmu su ne ke haifar da matsaloli, rudani, da rikicin yanki a tsakaninmu.”

Labarai Makamanta