Ministan Tsaro Ya Roƙi ‘Yan Najeriya Su Sanya Dakarun Soji Cikin Addu’a

Ministan tsaron ƙasar nan, Bashir Magashi, ya roƙi kiristoci da su yi ma sojojin ƙasar nan addu’a don kawo ƙarshen ta’addanci.

A wani jawabi da ya fitar ran Asabar ta hannun mai taimaka ma ministan kan harkokin yaɗa labarai, Mohammad Abdulkadri, Magashi ya roƙi mabiya addinin kirista da su yi amfani da wannan damar ta bikin ista su roƙi dawowar zaman lafiya a ƙasar nan.

Ministan ya ce, lokacin biki ista lokaci ne da yakamata mu roƙi taimakon Ubangiji ya shigo lamurran mu don samun hanyoyin magance ƙalubalen tsaro da muke fama da shi.

A kwanakin baya ne dai aka ruwaito Ministan tsaron na bayanin cewa tsaro ya samu a Najeriya, ya kuma bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Sanata Wamakko a ofishin shi dake birnin tarayya Abuja.

Labarai Makamanta