Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce mummunan fari da ba taɓa gani ba cikin gomma shekaru ya jefa miliyoyon yara cikin matsalar rashin abinci da ruwan sha a ƙasar Habasha wato Ethiopia.
A wani saƙo da UNICEF ɗin ya wallafa a shafinsa Tuwita ya ce da yawa daga cikin yaran na cikin hatsarin mutuwa sakamakon cutar cutar Tamowa.
Yankin gabashin Afirka na fama da mummnan farin da ba a taɓa gani ba cikin gwamman shekaru, bayan da aka kwashe damina biyar ba tare da samun girbe amfanin gona ba.
Lamarin da ya shafi mutane da dama tare da asarar dabbobi masu yawa, sakamakon rashin abinci da ruwan sha.
You must log in to post a comment.