Miliyan 56 APC Ta Ba ‘Yan Bindiga Domin Rike Daliban Jangeɓe – APGA

Shugaban jam’iyyar APGA a jihar Zamfara Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya zargi shugabannin jam’iyyar APC na jihar da bayar da naira miliyan 56 ga ‘yan fashi don kin sakin ‘yan matan Jangebe da aka sace.

Ya ce, manufar su ita ce yin zagon kasa game da kokarin samar da zaman lafiya na Gwamna Bello Mohammed Matawalle.

Shinkafi, wanda ya kasance dan takarar gwamna na APGA a 2019 a jihar Zamfara, ya yi wannan zargin ne yayin ganawa da manema labarai.

“Don haka, na kalubalanci ‘yan siyasa daga bangaren masu mulki da na jam’iyyun adawa da su sanya lambobin wayarsu zuwa binciken tsaro tun da ina da yakinin cewa labarin da zai fito daga wannan tsari zai zama abin birgewa,” in ji shi.

A cewarsa, binciken jami’an tsaro na wayoyin sirri na zababbun ‘yan siyasar ya kamata daga 25 ga Fabrairu zuwa lokacin da aka saki’ yan matan.

Da yake ci gaba, Shinkafi ya ce wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar APC a jihar ta Zamfara na matukar bukatar ganin cewa Matawalle ya gaza cika alkawarin da ya yi na sauya jihar, yana mai nuna cewa akwai bukatar jami’an tsaro su jajirce wajen takaita matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar.

Ya bukaci matasa da kar su yarda a yi amfani da su a matsayin ‘yan daba don kona Najeriya ta hanyar wasu’ yan siyasa marasa kishi da son kai, yana mai ba su shawarar su kara maida hankali kan gina kasa.

Shinkafi ya kuma yi kira ga gwamnati da ta fito da wani shiri da zai taimaka wajen karfafawa matasa ta hanyar samar musu da ayyukan yi.

Labarai Makamanta