Miliyan 113.2 Sun Yi Batan Dabo A Ma’aikatar Shari’a

Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na gwamnatin Tarayya ya fallasa yadda aka karkatar da naira miliyan 113.2 a Ma’aikatar Shari’a a cikin 2019.

Ofishin ministan Shari’a ya ce an ɗebi kuɗaɗen ne aka ce an biya wasu ayyuka da su, amma tsarin biyan kuɗin ya kauce wa dokar Kashe Kuɗaɗen Gwamnantin Tarayya.

An zare kuɗaɗen an biya ne ta hanyoyi daban-daban da su ka haɗa da biyan ‘yan kwangila tare da shirya bocar biyan kuɗaɗe da sauran hanyoyin da ba su dace ba.

Tashin farko aka saɗaɗa aka waske da wata naira miliyan 35.8. Amma dabarar da aka yi, sai aka karkasa ta gida 12, a cikin 2019, aka yi wa ma’aikata 12 watandar kuɗaɗen.

Labarai Makamanta