Mijin Sarauniyar Ingila Ya Mutu

Rahotanni daga fadar masarautar Ingila sun bayyana cewar Yarima Philip mijin Sarauniyar Ingila Elizabeth na II ya mutu yana da shekaru 99 a duniya kamar yadda fadar Buckingham Palace ta sanar a ranar Juma’a. An wallafa sanarwar rasuwarsa ne a shafin Twitter na fadar sarautar Ingila @RoyalFamily.

“Cikin tsananin jimami Mai Martaba Sarauniyar Ingila ta sanar da mutuwar mijinta abin kaunarta, Mai girma Yarima Philip, Duke na Edinburg,” a cewar sanarwar.

“Mai martaba ya mutu ne a safiyar ranar Juma’a a Fadar Windsor. “Iyalan gidan sarauta na alhinin mutuwarsa tare da dukkan mutane a fadin duniya. “Za a fitar da karin bayani a nan gaba dangane da yadda za’a gudanar da bikin binne gawarshi.

Yarima Philip Duke na Edinburgh, wanda ya shafe shekaru 73 yana auren Sarauniya Elizabeth ya ja baya daga ayyukansa na yi wa mutane hidima a shekarar 2017.

Shine basarake da ya fi dadewa kan karagar mulki a tarihin kasar Ingila. A watan Fabrairu an kwantar da shi a asibitin Sarki Edward VII da ke Central Landan bayan an sanar da cewa ‘baya jin dadi’.

Duk da cewa fadar ta ce rashin lafiyansa bata da alaka da cutar COVID-19, ba a sanar wa duniya ainihin abin da ke damunsa ba.

Bayan an yi masa aikin zuciya a asibitin St Bartholomew’s a Landan, an sallame shi a watan Maris. Philip sun haifi yara hudu tare da sarauniya Elizabeth, sunayensu Yarima Charles, Gimbiya Anne, Yarima Andrew da Yarima Edward.

Labarai Makamanta