Mayaudara Ne Ke Zuwa Neman Mu – Jaruma Zuwaira Abdussalam


Tsohuwar jaruma a Masana’antar finafinai ta kannywwod, Zuwaira Abdussalam ta bayyana Mazan da su ke zuwa neman “Yan fim da sunan za su aure su maza ne da su ke cike da yaudara.

Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar wakilin Jaridar Dimokuradiyya da ita dangane da zargin su da a ke yi na ruwan ido a Kan auren su, in da ta ke cewa

” Gaskiya ni ban yarda da wannan zancen ba, saboda mu Matan da mu ke yin fim in ka kula mafi yawancin Mazan da su ke zuwa neman mu su ne su ke zuwa da yaudara ba wai mu ne ba ma son auren Ba.”

Ta Kara da cewar “Domin Mazan da su ke kallon mu a fim su ke zuwa wajen mu su ne su ke zuwa da yaudara, saboda Sai su zo su nuna mana su wasu ne, amma daga baya Sai ka ga ba haka ba. Sai mutum ya canza daga matsayin sa ya zo da wata shiga ta daban, to da zarar an gano su Sai ka ga sun kauce, Kuma sai a daukar Matan ne su ke yaudara, don haka ba halin mu ba ne.”

Daga karshe ta yi kira da jama’a da su rinka yi musu adalci, domin su ma ‘ya’ ya ne kamar kowa, don haka su na bukatar a rinka yi musu uziri.

Labarai Makamanta