Mayakan ISWAP Sun Kaddamar Da Hari Kudancin Borno

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar wasu yan ta’adda da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne sun kai farmaki wani kauye a kudancin Jihar Borno.

‘Yan ta’addan sun farmaki kauyen Shallangba wanda ke kusa da Debiro a karamar hukumar Hawul, jihar Borno. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa mafarauta yan sa kai sun tarbi yan ta’addan, kuma sun fafata da juna yayin harin.

A cewar wata majiya, yan ta’addan sun kai hari ƙauyen a kan motoci, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi yayin da mutanen kauyen suke kokarin tserewa zuwa cikin jeji.

Wani mamban tawagar jami’an tsaron sa kai (CJTF) yace yan ta’addan sun fi karfin mafarautan, A ranar Lahadi da maraice, yan ta’addan suka kai hari ƙauyukan Debiro, wanda ya haɗa iyaka da kananan hukumomin Biu da Hawul na jihar Borno.

Labarai Makamanta