Mawaki Ali Jita Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Kano

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na nuna cewa yayin da jama’a ke ci gaba da hasashen yadda babban zaben kasar na 2023 zai kasance, an gano wani fostan yakin neman zabe na shahararren mawakin nan na masana’antar shirya fina-finai na Kannywood, Ali Isa Jita.

Fostan wanda abokiyar sana’arsa Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na Instagram, ya nuna cewa mawakin zai fito takarar kujerar gwamnan jihar Kano ne a zaben na 2023.

Sai dai kuma babu suna ko tambarin wata jam’iyyar siyasa a cikin hoton wanda ke dauke da rubutu kamar haka ‘hangen nesa, sha’awa, aiki Jita 2023, Ali Isa Jita don neman gwamna, jihar Kano, Insha Allah’.

Labarai Makamanta